Hebrews 3

1Don haka yanuwana tsarkaka, a bokan kira a samaniya. Yi la’akari da Yesu. wato Manzo da babban firist na shaidar bangaskiyarmu. 2Shi amintacce ne na Allah, wanda ya bashi hidima, kamar yadda Musa ya kasance amintacce a gidan Allah. 3Gama Yesu ya cancanci daukaka mafi girma fiye da ta Musa. Domin wanda ya gina gida, ya fi gidan nan daukaka. 4Gama kowane gida, akwai wanda ya gina shi, amma mai ginin komai shine Allah.

5Musa hakika amintaccen bawa ne a gidan Allah, yana ba da shaidar abubuwan da za su faru a nan gaba. 6Amma Almasihu shi Da ne mai mulki a gidan Allah. Mu ne gidansa idan mun rike begenmu da dukkan zuciyarmu.

7Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya fadi: ‘’Yau, Idan kun ji muryarsa, 8kada ku taurare zuciyarku kamar yadda ‘ya’yan isra’ila suka yi cikin tawaye a lokacin gwaji a jeji.

9A lokacin nan ne kakanninku suka yi mani tawaye, ta wurin gwada ni, bayan shekara arba’in suna ganin ayyukana. 10Saboda haka na yi bakin ciki da wannan tsarar, sai na ce,’ Kullum suna yawan bijirewa a zukatansu. Basu san tafarkuna ba.’ 11Don haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ba za su shiga cikin hutuna ba.”

12Ku yi hankali ‘yan’uwa kada a tarar da mummunar zuciya marar bangaskiya a tsakaninku, zuciya wadda ke juyawa daga Allah mai rai. 13Maimakon haka, ku karfafa juna a kowacce rana, muddun muna cikin wannan rana kada wani cikinku ya taurare zuciyarsa saboda yaudarar zunubi.

14Gama mun zama abokan aiki da Almasihu, idan mun rike begenmu cikinsa da karfi, daga farko zuwa karshe. 15Game da wannan, an fadi “Yau idan kun saurari muryarsa, kada ku taurare zuciyarku, kamar a kwanakin tawaye nan.”

16Su wanene suka ji muryar Allah suka yi tawaye? Ba wadanda Musa ya yi masu jagora daga Masar ba ne? 17Kuma da su wa Allah ya yi fushi shekara arba’in? Ba da wadanda suka yi zunubi ba ne, wadanda gawawwakinsu suka warwatsu a jeji? 18Da su wa Allah ya rantse ba za su shiga hutunsa ba? In ba wadanda suka yi masa rashin biyayya ba? Mun kuma gani cewa basu iya shiga hutunsa ba saboda rashin bangaskiyarsu.

19

Copyright information for HauULB